1. A bisa tsarin demokradiyya, shi ya zama gwarzo a zaben primary na jam’iyyarmu ta APC. Shugaba Baba Buhari ya bada dama a je a kara zabe, bai kuma sa hannunsa a ciki ba. An yi zabe mai inganci kuma Tinubu ne yayi nasara. Lalle kuwa dole mu mara masa baya.
2. Tinubu dinnan ya zamo haziqi ainun wurin tattalin arzikin kasa. Daga miliyan dari shida yau a birnin lagos ana samun kudin shiga biliyan hamsin a wata. Wannan ya samu ne daga jagorancin Tinubu. Yau an wayi gari har jirgin kasa na zirgi zirgan cikin jiha, mallakan gwamnatin lagos, yana nan yana aiki a lagos, wanda kuma duk Tinubu ne ya tsara shi tun ba yau ba. Tinubu ya Gina sabbin garuruwa a cikin lagos manya manya wanda har port an gina a wadannan garuruwan. Dangote ma da ya sha fama wurin gina refinery, lagos ne ta bashi daman samun duk ababen da yake bukata. Ya kuma ambata cewa ba don goyon bayan Tinubu ba, da bai yi nasara ba.
3. Mulkin kasan nan ba namu ne mu yan arewa kadai ba. Dole ne a riqa samun sauyi saboda zaman lafiya na kasa baki daya. An yi hadaka an kafa gwamnatin Baba Buhari kuma ya yi shekara takwas a kai. Bai kamata a samu mutanen arewa a matsayin marasa alkawari ba. Ya kamata suma mu mara musu baya su ma su taba. Akwai gobe, kuma gaba tafi baya yawa.
4. Duk da hargowan da aka ta yi, haka Tinubu ya toshe Kunnensa ya dauko dan arewa dan uwanmu Kashim Shettima ya saka shi a matsayin mataimakinsa don haka ne mafita a siyasar. Bai bari aqida na addini ya saba masa tunani ba.
5. Tinubu ya fi sauran chanchanta. Sanda aka basu dama a da, watanda suka yi da arzikin kasan suka sayar da duk ababen da muke tinqaho da su. Basu gina kowa ba basu gina komai ba. Shi kuwa Tinubu yana gina masallaci yana kuma gina masallata.
Jama’a a yi nazari.
Saqo daga Talban Bauchi Tahir Ibrahim Tahir, daya daga cikin directocin Committee na yaqin zaben Tinubu.